Kurkukun Kaddara 58-59


_*๐Ÿ’‹KURKUKUN ฦ˜ADDARA๐Ÿ’‹*_

*Dedicated To Aunty Kubra๐Ÿ’˜*

*Gargarษ—i!!!*

_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haษ—a mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haฦ™ฦ™ina!_

E58-59

๐Ÿ’ซ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ซ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ซ

*_ALBISHINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE, SHAHARARRA KUMA K’ASAITACIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WATO DR MAMAN YUSUF LIKITAR MATA SOKOTO TANA FARINCIKIN SANAR DAKU CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE A FADIN NIGERIA DA NIGER HARMA DA WASU K’ASASHEN BAKI DAYA, KU SANI A DADE ANAYI SAI GASKIYA KUMA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI , INA MARABA DA MASU SIYAN DAYA KO SARI_* 08133079957

*_munada zafafan kaya kamar haka ,_*๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป๐Ÿ‘‡๐Ÿป

*Hadin amarya budurwa ko zawara*

*Hadin uwar gida Mai taken (Maida tsohuwa yarinya)*

*Maijego package (virgin gain)* ๐Ÿ“ฆ

*Hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji*

*Sahihin maganin sanyi na Maza Dana Mata Wanda yake fatattakar sanyi cikin Dan lokaci*

*Maganin gyaran nono Wanda zai gyara maki nononki cikin Dan lokaci komai lalacewarsa*

*Maganin hips Wanda zaisa shape dinki ya fita kiyi kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji*

*Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko kiyi kiba yar dai dai misali kema adinga binki da kallo Idan kin juya Sam rama batayi ba yar uwa*

*Hadin mallaka ba boka ba malam , akwai taimakon da muke bayarwa ga Mai butsarin namiji Wanda cikin ruwan sanyi Zaki dinga juya abunki , haka akwai Hadi na musamman Wanda komai rowar namiji sai kin samu alkhairin a wajanshi,*

*Muna da kalolin gumbuna masu Saka ni’ima sha’awa da dandano*
*Kalolin garrika mash gyara gaban mace da jimawa ajiki*
*Kalolin Zuma masu saukar da ni’ima Nan take da gamsar da maigida*
*Kalolin tsumi Wanda cikin sauki zasu Baki ni’ima da dandano irin wadda akeso*
*Kalolin matsi Wanda suke ciko da gaban mace matse gaban mace da bata Wani irin dadi da dadano*
*Akwai set kala kala Wanda yawansh ya wuce na zayyanasu anan ga Mai bukatar kayana zata iya mun magana Kai tsaye ta hanyar Kiran ko Kuma Whatsapp* ๐Ÿ‘‰๐Ÿป 08133079957

*Muna dahuwar zabo ,dahuwar kaza ,dahuwar kifi ,dahuwar zuciya ,dahuwar Yan shila ,dahuwar tsoka Tara ,dahuwar Kwan mallaka, dambun nama ko na kaza Wanda yake saukar da ni’ima da jimawa sosai ajikin mace*

*Idan nace zan rubuta komai da komai to wannan page din ba zai isheni ba ,Amma ga masu sha’awar siyan kayana Zaku iya mun magana Kai tsaye ta wannan number, haka masu sha’awa su dinga ganin kalolin kayana a status sumin magana ta wannan number sai nayi seving numbers dinki ta hakan ne Zaku dinga ganin kalolin kayana idan na daura* 08133079957

*Ina maraba da Mai siyan Daya ko sari Dr maman Yusuf likitar mata sokoto*

 

 

 

Haฦ™iฦ™a Ta yi matuฦ™ar tafiya da hankalinsu, Kyakkyawar matashiyar budurwa, jawur da ita, Uniform ษ—in Jikinta Style ษ—in yasha banban da nasu, Ita nata gajeran skirt Launin Ja Ko laps ษ—inta bai rufe ba, fararen tsala tsalan cinyoyinta sun bayyana a suffarsu kamar ba’indiya, daga sama Coat ce launin Ja, daga Ciki ฦดar vest ce, Hannunta na Hagu na ruฦ™e da igiyar ฦ™atuwar backpack ษ—in data rataya saman shoulder ษ—inta.

yarinyar bata da ฦ™iba ko misฦ™ala zarratin, sai dai wani abu dake da matuฦ™ar jan hankali ajikinta, shi ne ฦ™irjinta, duk rashin ฦ™ibarta ฦ™irjinta a cike suke fam, Boobs ษ—inta tamkar zasu fasa rigar jikinta, tana da doguwar fuska, dara daran idanuwanta farare ฦ™al launin ocean blue, Jar sumar kanta anyi mata kitso guda biyu, bata da yawan gashi sai dai akwai tsayi, wutsiyoyin kitson sun sauko ta side by side na shoulders ษ—inta, hancinta hada nose ring golden colour, earrings ษ—inta na zallar gold ne, gefen wuyanta zanan tattoo ne na bindin ษ—awisu, Launika daban daban, A bunka ga farar fata zanan yayi bala’en yi mata kyau, daga gani yarinyar ฦดar gidan wani shege ce, mai ji da Naira, sai dai daga ganin fuskarta, ba ฦ™aramar wayayya bace, zai yi wuya tayi kunya a ido.

Hankulansu Haris gaba ษ—aya yana akanta, Har sai da taฦ™arasa saukowa daga saman benan, ta ษ—an dakata da yin tafiyar tana faman wurwuga manyan idanuwanta akan fuskokinsu, Sauran Sabbin Prisoners ษ—in dake a bayanta, Daga Cikinsu akwai wani matashin saurayi dogo twins ne shida ฦดar uwarshi, wuyansu na sanye da sarฦ™ar cross wanda ke nuni da addininsu, kyawawan gaske, Launin fatarsu kala ce mai tsada wadda ake kira da Chocolote, yadda kasan ษ—an wrestling haka ฦ™irar Jikinshi take, ga wata irin haษ—aษ—ษ—iyar sumar kai, Curly har ta gaban goshin kanshi, Uniform dinsu jajayene, Bayansu Akwai wani ฦ˜aramin yawo da bazai wuci shekara sha biyu ba, Albino ne (Zabiya) Hatta sumar kanshi Fara ce fat kamar hurhura, daga gani baida cikakken hankali don tunda suka faษ—o ษ—akin ya ke ta tsalle Yana dariya, Bayan su akwai wata Doguwar budurwa yadda kasan fatalwa, Bata da ฦ™iba ko kaษ—an, sai tsawo tubarkalla kamar qugunta zai karye, duk tsayin Danish To ga wadda ta taka shi, gwanin ban tsoro tana tafiya kamar macijiya, launin wankan tarwaษ—a ce ta ษ—aure guntuwar sumar kanta da ribbom,

Tashin sense, tsabar ruษ—u Ya hana su angel cewa komai sai kallon kallo suke yi a tsakaninsu da sabbin prisoners da aka kawo musu, Aranta tace wannan karan Hada Jinsin Aljanu aka bankaษ—o mana, Mun shiga ukun mu, Ashe Zaune bata ฦ™are ba,

Daga Cikin sabbin prisoners ษ—in akwai wata ฦดar ฦ™aramar yarinya da bazata wuci 10 years ba, Komai na jikinta sak irin na azeeza, banbancin shine ita azeeza tana da shekaru, girman jiki ke babu, Ita kuma wannan yarinya ce da gaske, Gata kyakkyawa itama, ga wani ฦ™ato mai manyan kumatu, da mazannai, Namiji ne baฦ™i wulik, yana tafiya tsokokin Jikin shi na motsawa, hatta ฦ™irjinshi acike yake kamar na mace, tashin hankali akwai gwarama fa,

a hankali Danish Ya sanya hannayen shi biyu ya sauke azeeza daga saman wuyan shi, Ya ajiye ta ฦ™asa, Yanayin fuskar kowannan su Ya canza, Lokacin da Sabbin prisoners ษ—in suka kammala shigowa ciki Su Goma sha takwas ne, Sanye Cikin Uniform jajaye kalar nasu Parveen, A jere suka tsaya cikin ษ—akin kamar masu jiran abasu Umarni, Kallon kallo su ke ta yi a tsakanin su dasu Deeja, Kowa Yasha Jinin Jikin shi, A hankali suka soma Jin takun tafiyar mutun daga can saman stair ษ—in, Da sauri Su angel suka kai idanuwansu kan Mai shigowa bakowa bace face*TSOHUWA ZAFREEN*cikin shigarta ta jajayen Kaya Ta rufe ko’ina na Jikinta, Idanuwanta kaษ—ai ne awaje, Yayin da hannayenta ke a ruke da sandar ta, daga bayanta Giants ne kusan su Uku, Gabza gabza, Masu ฦ™irar Samudawa, suna ฦ™arasa saukowa Cikin ษ—akin, Da sauri Danish Yace masu Parveen su gaishe ta, Atare suka ษ—an russina Cikin girmamawa suke gaishe ta, Wani abun mamaki Mutun ษ—aya ce bata russina mata ba, Saboda ฦ™arfin hali irin na angel hada goya hannayenta saman ฦ™irjinta, Fuskarta babu annuri, don ta gane cewa itace tsohuwa zafreen, Ba ta yi tsammanin zata ankara da ita ba, Sai ji tayi tace”Ke baki Iya gaisuwa bane”? Cikin ฦ™arfin hali angel tace”Na iya, Ina kwana,”

Al’ajabi ne ya kama Zafreen, Hankalin Danish kuwa idan yai dubu toh ya tashi, da ido yake yi ma angel magana akan ta duฦ™a ta gaishe da ita, amma ฦดar tahalikar nan sai tayi kamar bata gan shi ba, hada ฦ™oฦ™arin ษ—aure fuska idonta na kallon ฦ™asa,

Da kakkausar Murya Tsohuwa zafreen tace”Ki gaishe ni kamar yarda sauran ฦดan uwanki suka yi mini” Cikin jin fargaba da ฦ™arfin hali angel tace”wuya na ke ciwo, bazan Iya russina kai na ba, amma ki gafarce ni”

Tsabar mamaki yasa Idon kowa ya koma kan Angel, Hatta Giants dake a bayan Zafreen Acike suke da al’ajabin maganar Angel, Idan ka kalli fuskarta zaka ga ta ษ—aure ta tamau, kuma babu alamun wuyan nata na ciwo, ita kanta amma a firgice take, saboda wani irin mugun tsora da take ji, kuma da gangan taฦ™i russina mata, Saboda ba ta yi Niyya ba ne, don bata ga dalilin da zaisa ta ฦ™asฦ™antar da kanta wurin gaishe da tsohuwa Zafreen ba.

Jinjina kai tsohuwa zafreen tayi babu alamun ta fusata, Sai ma ta miฦ™a mata hannu don su gaisa, a ruษ—e angel ta kalli tafin hannun zafreen dake a sanye cikin jar safa, Wani irin fagaba taji

“am happy to see your face, my granddaughter, ฦ˜warin gwiwarki ya burge ni, tun da nake a duniyar nan ban ta6a ganin mahalukin da baya jin shakkar Yi min magana irin ki ba, ga ki ฦ™arama Kamar insa ฦ™afa in take” Jin wannan magana yasa angel taji hankalinta ya ษ—an kwanta, har ta samun damar ษ—aura hannunta acikin na tsohuwa tsaffin, Sosai ta ruฦ™e hannun angel acikin nata, Kafin daga bisani ta sakar mata hannunta,

Cikin ฦ™asaita Ta Juya baya ta kalli Giants da ta zo dasu, Da hannu ta yi masu magana ba tare da ta furta musu a baki ba, Yatsu Biyar ta watsa musu sau biyu, Gaba ษ—aya su angel suka shiga ruษ—ani sunyi tsammanin wani mugun abun zata yi musu sakamakon Abunda Angel tayi mata, Amma sai suka Giant Sun Kalli Sabbin prisoners da suka zo dasu, Da hannu Suka nuna mutun biyar na farko da suka fara shigowa, su ka yi musu alamar su tsaya a ษ—akin, Sauran Goman Cikin su Da hannu su kayi musu alamar su wuce su tafi, A matuฦ™ar ruษ—e Su angel suke kallon su Cike da mamakin Ina za’a kai Mutun Goma da Giants suka ware? kenan an fasa ajiye su a ษ—akin su? can kuma ta tuna da maganar da Batool ta ta6a faษ—a mata na cewa Akwai wasu 6angarorin da prisoners suke rayuwa a gidan kurkukun basu ka ษ—ai bane, wata’ฦ™il can za’a kai su.

A jere mutun Goman nan suka nufi saman Benan zasu koma, Christian ษ—in nan Namiji Ya fasa wata irin ฦ™ara da taja hankalinsu, da gudu yabi bayan waษ—anda aka tafi dasu, Sai dai bai kai ga ฦ™arasawa ba, Giants suka Damฦ™o hannun shi, sosai idanuwanshi suke fitar da hawaye Yayin da yake miฦ™a hannu yana nuna ฦดar uwarshi mace, Yana faษ—in”My twin sister pls kada ku raba ni da ita, bazan iya rayuwa babu ita ba, ” Fashewa da kuka ฦดar uwar tashi ta yi kamar ranta zai fita, da gudu ta dawo ta faษ—a jikinshi ta ฦ™anฦ™ameta, Kamar zai maida ta Cikinsa, wani irin tausayin su ne ya kama su angel, azeeza tuni ta fara yi musu kuka saboda sun yi matuฦ™ar ta6a mata zuciyarta, bayin Allah Kamanninsu sak iri ษ—aya, Daga gani suna matuฦ™ar ฦ™aunar junan su, saboda rashin Imani na Giants suka sa ฦ™arfi wurin raba su da juna, Su ka tasa ฦ™eyar macen gaba suka haura saman benan, Sai kuka take tana faษ—in”My twin bro, Ka kula min da kan ka, Duk inda za’a kai ni zan dawo wurin ka,” shima yana kuka yana kiran sunanta, Ahaka har aka fuce da ita” Bayan fitar su ษ—akin yai tsit Ya rage Saura Su Angel da tsohuwa Zafreen sai mutun biyar da aka Bar musu cikin sabbin prisoners, Haฦ™ika Tagwayen sunyi matuฦ™ar ta6a Zuciyoyin su, Namijin sai share kwalla yake yi, idanuwanshi sun yi jawur dasu, ga wata irin zufa dake tsastsafo mishi, Allah kaษ—ai yasan irin raษ—aษ—in da yake ji acikin zuciyarshi, An raba shi da twin sister ษ—inshi, Giant sun yi yankan ฦ™auna.

Gyaran murya tsohuwa zafreen ta yi musu kowa Ya shiga natsuwarshi, Cikin harshen turanci ta soma Yi musu magana

“Ina fata tsohuwa Tamira ta yi maku bayanin komai a dangane dani, ba sai na maimaita ba,” Har suna haษ—a baki wurin ce mata eh,

Jinjina kai tayi Yayin da take kallonsu ษ—aya bayan ษ—aya, kafin ta tsaida Tsoffin idanuwanta kan fuskar angel,

“Sai dai ga dukkan alamu akwai waษ—anda basu san wacece ni ba, Amma asannu zasu fahimta”

Ta ฦ™arasa maganar tare da juyawa ta kalli Sabbin prisoners da aka Bar musu tace”Ya rage naku, Ku zauna lafiya ko akasin hakan, Bata shafe ni ba, zan dinga zuwa akai akai ina duba ku, A koda yaushe ku kasance Cikin shiri”

A hankali ta soma ja da baya Still idonta akan Angel, Kafin ta ษ—auke su tare da juyawa ta nufi stairs ta haye, Giants su ka take musu baya, Suna jiyo datse ฦ™opar ษ—akin, Nan fa kowannan su Ya shiga sauke ajiyar zuciya, don ba ฦ™aramin shakkarta suke ji ba,

Sai lokacin su Haris suka samu damar yin magana

“Wannan wani irin rashin imani ne? Don me za’a raba shi da ฦดar uwarshi? Bayan akwai sauran gadajen da kowannan su zai samu wurin kwana, Ni bansan me ke damun waษ—annan mutanan ba, tsabar zalunci ne kawai” Haris ne yae magana yana mai jan tsoki, Azeeza tace ni wlh tausayi suka bani bayin Allah, hakanan an raba su”

Angel ta shiga ruษ—ani, Ita damuwarta ina za’a kai sauran toh? Ga kuma gadajen su A ajiye, Allah dai yasa ba wani mugun abun za’ayi musu ba, bakowa tafi jima tausayi ba face christian ษ—in nan, Ya yi tsaye hawaye ta ko’ina akan fuskarsa.

Danish ne yai ฦ™oฦ™arin zuwa wurin shi Ya janyo shi tare da rungume shi yana lallashinsa, Cikin shessheฦ™ar kuka yake faษ—a mishi cewa ฦดar uwarshi, tun da suka taso atare suke rayuwa komai atare suke yi, basu ta6a rabuwa ba, Amma yau An raba shi da ita,” daฦ™yar Danish ya samu Ya lallashe shi, Har ya daina kukan, Tukunna Ya raba jikin su,

Tun da suka shigo ษ—akin Yaron nan da aka bar musu zabiya, Sai tsalle Yake Yi yana dariya, babu wanda ya lura dashi saboda Halin da suka shiga, Ya haye saman gadajensu Yana ta ษ—aukar fululluka yana watsar dasu ฦ™asa Hada bargunansu.

“Hey, y’all! my name is Unaiza, and i’m excited to get to know u all.”

Da sauri suka kalli bakin mai magana, wata irin zazzaฦ™ar murya mai cike da kwarkwasa da duniyanci, Bakowa bace face ฦณar madarar nan, da alama taji sunyi tsit basu tarbesu ba, Shiyasa tayi fara yi musu magana, ae daga ganinta wayayyiya ce, Murmushin yaฦ™e kowannansu ya sakar mata, Batare da sunce komai ba, ta kuma cewa

“It seems like we’re not welcome at all” Jin wannan maganar yasa Danish Yin ฦ™oฦ™arin yi mata magana

“it’s not like that, We welcome you with open arms. We are excited to have you here and look forward to getting to know you. You are highly welcome here”

Fuskar shi ษ—auke da murmushi ya ฦ™arasa maganar, Yana yi musu nuni da gadajen su, don su shugo ciki su zauna.

shu’umin murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, irin na tatattun ฦดan iska, Ba zato ba tsammani, su angel suka ga ta nufi Danish Tana ฦ™arasawa gabanshi Ta sanya hannu biyu Tayi hugging ษ—inshi ajikinta, Cikin harshen turancin dake nuni da ฦ™warewar ta ta furta”Tayi matuฦ™ar jin daษ—in haษ—uwa da shi, tana fata za’a kar6e su hannu bibbiyu,”

Ran angel ya 6aci da sauri ta nufi inda suke atsaye, Suma sauran suka bi bayanta, Tana ฦ™arasawa gabansu ta sanya hannu Ta ruฦ™o damtsen hannun Danish Ta janye shi daga Jikin yarinyar, ta dinga jefa mata harara, Amma ko ajikinta sai ma ta sakar mata ฦ™ayataccen murmushi tare da miฦ™a mata hannu don su gaisa

“Hi, Am unaizah ฦดar gidan daddy, can i know u”? Ta jefa ma angel tambayar, Yatsina fuska angel ta yi, Kamar bazata tanka mata ba, Sai kuma tace”My name is Unaisah, Amma daddyna Yana kira na Angel, shine sunan da kowa Yake kira na” Dariya su ka ga ta saki tare da cewa”Wow, sunan mu yae shige dana juna, banbancin kawai harafin ฦ™arshe ne, ina fata zamu zama abokai” Da hausa tayi maganar amma sai ka rantse da Allah da turanci tayi ta, Saboda Yadda take furta ta, daga gani baturiyace amma ta iya hausa ba laifi,’

Murmushin yaฦ™e angel ta sakar mata tare da cewa”why not, tun da zama ya haษ—u mu wuri ษ—aya” murmushi ta kuma saki tana kallon fuskokin su Tace Idan ba damu tana son su gabatar mata da kansu, batare da sun Yi mata musu ba, ษ—aya bayan ษ—aya Kowannan su Ya gabatar mata da kanshi, koda a kazo kan Danish Yana yi mata bayani dangane dashi har wani lumshe ido take yi tana kallonshi, ran angel ya gama 6aci gani take kamar an kawo musu annoba ne, saboda babu natsuwa atare da yarinyar, bayan sun gama da kansu, Haris ya kalli sauran sabbin prisoners ษ—in yace”saura ku ya rage ku faษ—a mana sunayen ku, sannan muna son musan daga ina ku ke”_

ฦ˜aramar yarinyar nan ce ta fara Yi musu magana tace sunanta *JAMIMAH* Itama Prisoner ce a gidan kurkukun ta taso shekararta Goma cuf aduniya,” Bayan Jamima Ta kammala gabatar musu da kanta, Wannan Doguwar mai zubin Taliyar indomi Ta faษ—a musu cewa”ita Sunanta *SARAH* shekararta, Sha bakwai, Itama rainon kurkukun ฦ™addara ce” Jinjina kai su kayi yayin da suka maida dubansu ga kirista ษ—in nan suka ce mashi Ya faษ—a musu wanene shi, Cikin sanyin murya yace musu Sunan shi*GABRIEL* twin sister ษ—in shi kuma sunanta *GABRIELA* shekararsu goma sha bakwai,” su angel sun yi mamakin jin shekarun su ashe duk Yara ne, Girman Jikine kawai, Naufal yace”rainon kurkukune ku ma Ko kuwa daga waje aka kawo ku”? Gabriel yace mishi bazai iya tuna komai dangane da rayuwarsu ta baya ba, shi dai kawai a bunda zai iya tunawa twins ne su, yana matuฦ™ar ฦ™aunar ฦดar uwarshi itama tana son shi, tare suka taso basu ta6a rabuwa ba”

Maganar shi ta ษ—aurewa Angel kai, ga dukkan alamu suma tagwayen ba rainon kurkuku bane, daga waje aka zo su, Saboda babu addini agidan kurkukun ฦ™addara, Su kuma Akwai sarฦ™ar cross a wuyansu, hakan na nufin An canza musu tunaninsu ne,

Gaba ษ—aya sun manta da mutun ษ—aya daya rage basu su tambayi wanene shi ba, Kowa ya shafa’a da ษ—an ta halikin nan, Sai da Parveen ta tuna da Abincinsu, Da sauri ta waiwaya baya don ta kalli Kayan abinci, Ras taji gaban ta ya faษ—i ganin Mahaukacin yaron nan zuฦ™unne gaban faranti Ya ษ—auki Chicken shawarma Yana turawa abaki, rabi na shiga rabi na zubewa ฦ™asa duk ya cakalkala ta, ga kuma Bargunansu daya wurgo ฦ™asa da fululluka, Da ฦ™arfi Ta ambaci”Innalallahi! ” gaba ษ—aya suka kalle ta, Ganin Tana kallon saitin dining carpet ษ—insu Yasa suma suka kalli wurin, Da gudun gaske parveen ta nufi yaron ta shaฦ™o wuyan rigarshi Ta wurgar dashi gefe ษ—aya, Ya faษ—i ฦ™asa kanshi ya bugu, Maimakon yayi kuka sai ya kama Dariya Yana Wuntsila ฦ™afafuwanshi, Rai a6ace Parveen ta shaฦ™o wuyanshi tana faษ—in”Wanene kai?daga zuwa yau zaka fara Yi mana hauka? kana da hankali Kuwa…..” bata kai ฦ™arshen maganar ba, sakamakon jin saukar Yawun daya watsa mata akan fuskarta, tsabar fusata yasa ta kikkifa mishi maru ka, ya dinga dariya ba ฦ™aฦ™ฦ™autawa, daga gani jaki ne bai jin bugu.

Hankalinsu yae matuฦ™ar tashi, saboda sun fahimci cewa Yaron yana da ta6in hankali, Mahaukaci ne aka kawo musu,

“Parveen ki daina bugun shi, Baki ga yaro bane”? Azeeza ce tai mata magana, Rai a6ace tace”Babu ruwana da yaro ne, Ubanshi zanci, har ni zai watsa wa miyau a fuska”? Da alama ta fusata, Rigarshi ta damฦ™o ta goge miyan daya watsa mata a face ษ—inta, duk da haka bata ฦ™yale shi ba, sai da ta sanya hannu ta dunguri kanshi, Kafin ta miฦ™e ta nufi toilet don ta wanke fuskarta, badajimawa ba Sai ga parveen ta dawo Cikin ษ—akin fuskarta ษ—auke da lemar ruwa, Sai Jifar yaron take yi da harara kamar ฦ™wayar idon zasu faษ—o ฦ™asa.

Deeja tace”Mun shiga uku, tamu ta same mu, Yanzu haka zamu rayu da wannan Ta6a66an? Naufal yace”Bazamu zuba mishi ido ba, Dole mu koya mishi hankali,” tsoki haris yaja batare daya ce komai ba,

Danish ne yace da sauran”Idan kuna jin yunwa ga abinci nan, Idan zaku huta ga beds ษ—inku nan, sannan…….” bai ฦ™arasa ba yaษ—an kalli ฦ™opar shiga sashen toilet ษ—insu yace”Game buฦ™atar watsa ruwa ko yin wani uziri wannan ฦ™opar zaku bi, Anan toilets ษ—in mu su ke” Yana magana hankalin shi na akan Matashiyar yarinyar nan, dake ta kallon shi tana faman cizon pink lips ษ—inta, ran angel idan yai dubu ya 6aci, bakomai yafi ฦ™ona mata rai ba face ganin yadda take kallon Danish tana cizon le6e, tarasa gane me hakan ke nufi, to ko dai halittarta ce ahaka? Ko kuwa wani sabon salon iskancin ne”?

“Bana jin yunwa, I need to take bath, before in kwanta In huta” ฦณar gidan daddy ce tayi maganar tana ฦ™oฦ™arin sauke School bag ษ—inta, Idon kowa na akanta, Miฦ™a ma Danish Backpack ษ—in tai tare da cewa”Ka ajiye min ita, sannan ka raka ki toilet ษ—in, bazan iya ganewa ba” Wani irin kallon harara angel take jefa ma Danish, duk yasha jinin jikin shi, Sam ya kasa kar6ar jakar Unaiza, Sai angel ce ta kar6e jakar tace”Zan ajiye maki ita, sannan zan raka ki toilet ษ—in, idan ma kinaso har cuษ—a maki baya zan Iya yi” Girgiza kai Unaiza tae tana fadin”No, bana so, ki dai ajiye min back pack ษ—in, Shi sai ya raka ni toilet ษ—in” mamaki ne ya kama angel, aranta tace”that’s impossible, kinzo da bidi’a,” Kar6ar jakar tayi daga hannun unaiza taje ta ajiye mata ita gefen donta mai ษ—auke da no 16, juyowar da za ta yi, karaf idanuwanta suka sauka akan Unaiza da ke ฦ™oฦ™arin cire Coat ษ—inta, Bakomai ne ya faษ—ar mata da gaba ba, face ฦ˜irjin Unaiza, Musamman da ta ฦ™arasa Cire rigar Hankalin Kowa Ya koma kansu, Kamar babu riga ajikinta saboda Yadda surar su ta bayyana ajikin vest din, Manya manya dasu kamar balan balan, shatun nipples ษ—in sun fito sosai, kamar zasu huda ta, gata yarinya amma tubarkalla, Allah yayita da boobs, ”

Kwanciyar hankali ya ฦ™arewa angel, Kishi ne ya addabi zuciyarta, kodan hada ฦ™arin ita bata da su ne, Oho dai,

Bayan Unaiza ta ษ—ebe Coat ษ—in Ta miฦ™a ma Danish tace Ya ruฦ™e mata, Hannun shi na kerma ya ruฦ™eta, wani irin ฦ™amshi ne ke fita jikin coat ษ—inta,” hannayenta ta ษ—aura saman gajeran skirt ษ—inta, Waro ido angel tae baki a sake take kallon ikon Allah, Cire shi tae ya rage daga ita sai Short na mata, ”

duk su naufal suna a tsaye suna kallon ikon Allah, Miฦ™e ma Danish Skirt ษ—in ta yi”Ka ajiye min su” Kafin yai yunฦ™urin kar6ar skirt ษ—in angel tai saurin komawa wurinsu ta sanya hannu ta kar6i skirt din ta kuma ฦ™waci coat ษ—in dake a hannun Danish, Fuskarta a ษ—aure ta nufi akwatinsu ta sanya mata su a ciki, Kafin ta dawo ta tsaya agefen Danish,

“Muje ka raka ni toile ษ—in” ta yi maganar tana ฦ™oฦ™arin ruฦ™o hannunshi, Angel tae saurin ka6e mata hannun”Ni zan raka ki,” Bata jira amsar da unaiza zata bata ba, Taja hannunta, ta wuce da ita zuwa sashen toilet ษ—insu, sai bayan da suka shige, azeeza da parveen suka kalli juna, Alamar mamaki, sufa sunga abunda basu ta6a ganin irin shi ba, tun da ko tsohuwa nata azube suke kamar silifas, Cikinsu kuwa ba wadda ta ke da su irin na ฦดar gidan daddy, har ฦ™wara waษ—an da suka fara manyanta, Sune ya fara fito mawa, amma ita ko wannan ฦดar shilan ฦ™irjinta sunfi ฦ™arfin jikinta da shekarunta.

“Gabriel, banji kace komai ba”? Danish ne yae mishi magana ganin yayi tsaye bai motsa ba shi da sauran ฦดan uwan nashi, Cikin sanyin murya yace”Inaso na kwanta, saboda kaina ciwo yake yi min” Nuna mashi gadonshi danish yae da hannu, Yace mashi thanks kafin Ya nufi gadon, Sai da ya fara cire coat ษ—insa, Ya ษ—aura ta gefe, Sannan ya haye gadon ya kwanta,

Kallon Jamima su kayi ฦดar ฦ™aramar yarinyar nan, parveen ta raya aranta cewa”Wannan dai rainonta zamuyi da alama” Haris ne yace da ita”Kefa? Zaki kwanta ko xaki ci abinci” Ta6e baki ta ษ—anyi kafin tace”Yunwa nake ji,” Deeja tace”amma ke kike yin wanka da kanki”? ฦŠaga mata kai tayi”Eh, inayi yanzu, amma sai ana cuta min bayana saboda hannu na bai kai wa” Murmushine ya bayyana akan fuskokinsu, don ba ฦ™aramin burgesu tayi ba, gata ฦดar kyakkyawa da ita, Hibba tace”idan ma kinaso har wankan sai muyi maki,” dariya tasaki tare da sanya tafin hannayenta ta rufe fuskarta, alamar taji kunya.

Ruฦ™o hannunta Haris yae acikin nashi yace”muje muci abinci ko”? Tace mishi eh, ” mubeen yace”to itafa Wannan bamu ji ra’ayinta ba, ” yae maganar yana nuna Sarah dake atsaye Ta ruฦ™e qugu, Yatsina fuska Ta ษ—anyi can kuma saita ฦ™aฦ™aro murmushi tace”Nima bana Jin yunwa, zan kwanta na huta ne” tae maganar tare da juya ta nufi gadajensu, ฦŠaya bayan ษ—aya take binsu da kallo, a sukwane Ta juyo ta kalle su Deeja tace”wai a ina zata kwanta ne”?

Nan take su ka fahimci cewa Ta raino gadon ne, Wato yayi mata ฦ™anฦ™anta, Hannah tace”Acan inda kuka Baro, a saman Ina ki ke kwana ne”? ta6e baki Sarah ta yi Ba tare da ta bata amsa ba, Ta maida idonta kan gadon, Ta curo bargon saman shi, Ta shimfiษ—ashi a ฦ™asa, ta ษ—auko pillow ta jefa, Kafin ta cire coat ษ—in Jikinta ta ษ—aura a ฦ™asa, Ta faษ—a sama gadon ta kwanta.

A bunda ya faru bayan Angel ta raka ฦดar gidan daddy toilet, suna shiga ciki taja burki ta tsaya Tana faman zazzare blue eyes ษ—inta haษ—i da yatsina fuska, Angel tace”Ni xan Koma, ayi wanka lafiya” har zata juya muryar Unaiza ta dakatar da ita

“Nifa ban fahimta ba, Ina bathtub yake ne? tana nufin (kwamin wanka) Wannan wani irin toilet ne kamar na Marasa galihu” Tsabar mamaki yasa angel sakin baki kamar sakarya tana kallonta, Daฦ™yar ta iya buษ—e baki tace”ba mu da bathtub, Iya a bunda idonki suka gane maki acikin toilet din su muke dasu, Ga Shower nan, Sai kuma bokiti, can kuma Soso ne da sabulu,” aruษ—e unaiza tace”that’s Impossible, ae ni bana sharing soson wanka, Kuma bana wanka in ba a cikin bathtub ba, I can’t stay here i wanna go home, cos daddy ba haka Ya kwatanta min school ษ—in ba, Yace min fa komai irin na Gidan mu ne, but why naga banbanci”? tamkar zata fashe da kuka tayi maganar, har saida gaban angel ya faษ—i jin abunda tace, Wato ita duk a tunaninta School ce aka kawota batasan cewa Prison bane, To me hakan ke nufi? Kodai mahaifinta ne ya yi mata ฦ™arya kan cewa za’a kawo ta makaranta! Tashin hankali Sai lokacin angel ta tuna da irin uniform ษ—inta na gayu, dama ta yi mamakin ganinta da haษ—aษ—ษ—un takalma ฦดan ฦ™waras ฦ™waras, Ga gajeran skirt na gayu, Ga kuma ฦ™atuwar School bag Ta goyo, Tabษ—ijancan, In dai a bunda take hasashe ya tabbata to kuwa Iyayenta sun Cuce ta, Mamaki Ya hana angel cewa komai, taya akai basu gusar mata da hankalinta ba? Kamar yarda aka yi ma Gabriel? Ko kuwa sihirin ne bai kama Jikinta ba?

ta yi zurfi acikin tunaninta muryar unaiza ta katse ta”Pls talk to me! Ni ban fahimci komai ba, game da school din nan,” tashin hankali ne Ya bayyana ฦ™arara akan fuskar angel, miryarta na ษ—an rawa tace da unaiza”wacece ke? Dama ke ba rainon Kurkuku bace”? Waro ido tae tare da maimaita sunan prison da angel ta faษ—i, Ba don ta fahimci me hakan ke nufi ba,

“Ban fahimce ki ba, Naji kince prison, Nifa daddyna yace dani xai sanya ni a high school Na south korea, saboda inason kallon drama ษ—in su komai nasu yana ฦ™ayatar dani, Daddyna yana yi min komai nake so, shi ne Da kanshi, Ya sama min admission a school ษ—in nan, a gida aka kawo min uniform na sanya ajiki na……” unaiza bata ฦ™arasa maganarta ba, Angel ta ษ—aura hannunta akai,! Irin ta shiga ukun nan, fito wa ta yi daga Cikin toilet ษ—in Ta tsaya daga waje tana ambaton”Innallahi wa’inna ilaihirraji’un”! da sauri ฦดar gidan daddy ta biyo bayan angel, baiwar Allah duk ta ruษ—e ta rasa gane me angel ke nufi,

“Pls tell me the truth Ko ba school bane nan ษ—in? I ave to know” wani irin kallon tausayi angel ke binta dashi, muryarta kamar ta mashayin giya tace”Zaki iya tuna Ta ina aka kawo ki Nan” girgiza kai tayi”I can’t remember, Ni dai nasan time da masu aikin gidan mu, suka taimaka min nayi wanka na sanya uniform da daddyna ya bani, so bayan nan sun rakoni zuwa wurin da motocin bodyguards ษ—ina su ke, sun buษ—e min mota, Na shiga Ciki na zauna, ina ta farin ciki, duk na qagara mu ฦ™arasa Airport sai bacci ya ษ—auke ni, daga nan ban ฦ™ara tuna komai ba, sai dai na ganni Acikin School ษ—in nan tare da sauran students din da muka zo da su” Tana magana tana yatsina fuska daga gani ษ—abi’arta ce yin hakan,

Jinjina kai angel tae yayin da take kallonta, haฦ™ika ta yi mamakin da basu canza mata tunaninta ba, tun da har ta iya faษ—in yadda aka kawota Cikinsu, tabbas kowanene Ubanta ba ฦ™aramin Mugu bane, Azzalumi, Wato shi wayau yayi mata ya fake da cewa za’a kaita Sk don ta yi karatu batasan cewa Sadaukar da ita ya yi ba zuwa Gidan Kurkukun ฦ™addara, don biyan wata buฦ™ata tashi, Rayuwarta abun tausayi baiwar Allah, Sai da aka gama sangartata, Daga gani an gama jiyar da ita duk wani daษ—i na duniyar nan kafin aka tsamota daga aljannar duniya aka kawota gidan kurkukun ฦ™addara,

Ganin irin kallon da angel take binta dashi ne yasa tace”Pls Ke nake jira ki bani amsa,” A ฦ™agare tayi maganar,

“Ya sunan mahaifinki? Kuma wanene shi”? Muryarta A disashe tace”Ae ni bansan real name nashi ba, na dai san ana kiran shi Jan wuya…” bata ฦ™arasa maganar ba angel ta katse ta da cewa”Ba ki ta6a zuwa school bane? Da wani suna kike amfani”? Ta bata amsa da cewa”ni tunda na taso ban ta6a zuwa school ba, daddyna bayaso ina shan wahala, A gida ake koya min karatu, yanzu ma don na kwallafa raine akan inason zuwa south korea karatu shine yace zai sani….”

Jinjina kai angel tae kafin tace”Amma awace ฦ™asa ku ke zaune duk da naji kina magana da yare biyu, hausa da turanci so na kasa gane wani jinsi kike”

Wannan karan tamkar zata fashe mata da kuka ta yi maganar don ta gaji da tsayuwa,

“My dad is from Nigeria and my mom is from England. I’ve never been to Nigeria, and I don’t know my dad’s hometown or his job, Ni da Mommyna ne kawai muke rayuwa a england sai ฦดan Aikin gidan mu, amma yana yawan zuwa kawo min ziyara daga Nigeria”

Hankalin angel ya ฦ™ara tashi, daฦ™yar tace mata yanzu kiyi haฦ™uri kiyi wankan idan kin kammala zanyi maki bayanin komai” Girgiza kai tayi”ae bazan iya wanka awannan toilet din ba, saboda ba irin na gidanmu bane, ni nasaba acikin bathtub nake yi, kuma masu aikin gidan mu ne suke taimaka min wurin yin wankan”

Kallon ta kawai angel ke yi, Iya cutuwa dai an Cuci yarinyar nan, tama rasa taya zata fahimtar da ita cewa Nan kurkuku ne, ba high school ta ฦ™asar korea ba? Zaiyi wuya ta fahimce ta, babbar matsalar irinsu Suna da ฦ™arancin imani, sannan basu da tawakkali, Tana iya ta faษ—a mata azo asamu matsala, Ya za tayi da ita?

Yayin da su Angel suke a sashen toilet dinsu ita da ฦดar gidan daddy, Su kuma can ษ—aki suna fama da wannan mahaukacin Yaron, abunda ya faru Suna ฦ™oฦ™arin zuwa suci abinci, Eve tace dasu,

“Wai nikam Ina Yaron nan yake ne”? Kafin wani ya buษ—e baki ya bata amsa suka Ji ฦ™arar karyewar wani abu acikin kunnuwansu, Agigice suka kai idanuwansu wurin da suka Jiyo sautin ฦ™arar, ransu yae mutuฦ™ar 6aci ganin Irin uwar 6arnar da Yaron yayi musu, Gaba ษ—aya Ya kado da cake ษ—insu ฦ™asa, Table ษ—in Ya 6alle, Cake ษ—in ya ฦ™undumo kasa Ya tarwatse, hakan bai ishe shi ba, sai da ya hau saman Cake ษ—in Ya dinga duma hannuwanshi aciki Yana Kwaso shi Yana turawa abakinsa, duk ya 6ata uniform ษ—in jikin shi da cake ษ—in, A ฦ™arshe ma sai ya hau saman Cake ษ—in ya dinga burgima yana dariya, a fusace parveen ta nufi inda yake, Haris da Danish suna ta ฦ™oฦ™arin dakatar da ita akan kada ta buge shi, amma ina ko waiwayon su bata yi ba, wata irin damฦ™a takai ma wuyan rigar shi, ta ษ—ago dashi ta daddage ta buga kanshi a ฦ™asa, azabar zafi yasa shi fashewa da kuka mai tsiwar gaske, tana huci tace”Shege ashe kana jin bugu, ae nayi tunanin kurma ne kai” Sautin kukan yaron ne ya karaษ—e kunnuwansu angel dake a sashen toilet ษ—insu, da gudu suka nufi ษ—akin suna shugowa suka ci burki suna kallon Yaron dake ta kuka, Hatta gabriel dake kwance yana bacci shi da Sarah sai da suka farka saboda sautin kukan fitinannan Yaron, An rasa me lallashin shi acikin su, haushin shi suke Ji, Ya baฦ™anta musu rai, duk irin yadda suka ฦ™walla fa ransu ga son cin cake ษ—in nan ya tarwatsa komai, Farin Cikinsu Ya gushe, Har ga Allah basu Ji daษ—in zuwan prisoners ษ—in nan ba, Saboda mutun biyun nan dake acikinsu, Mahaukacin yaron nan da Angel ta sanyawa suna Majnun saboda Yaฦ™i faษ—a musu sunanshi, Sai kuma Unaiza ฦดar gidan daddy, A ranar Bayan Danish ya lallashi Yaron Yaje dashi toilet ya wanke mishi Jikin shi Da uniform ษ—inshi da ya 6ata da cake, Ya shanya su saman igiyar toilet ษ—insu, ya ษ—auko bargo Ya ฦ™udundune shi ajiki yakai shi Daki ya kwantar dashi saman gadon shi, Cikin ฦ™anฦ™ani lokaci bacci yayi awon gaba dashi, Hankalinsu har ya kwanta, ashe ฦ™ura bata lafa ba, Sun gama shan wahalar gyara ษ—akin nasu da ya 6ata musu ya hargitsa komai, Suna ฦ™oฦ™arin zama su huta, Unaiza tace musu Yunwa take ji, Suka ce mata Ga abinci can saman dining carpet ษ—insu taje taci, Saboda damuwa ma yasa babu wanda ya waiwayi abinci acikin su, Sai wannan ฦ™aramar yarinyar jamimah ita kaษ—ai ta zauna tana ci.

Ita ko Unaiza ฦดar gidan daddy ta ce musu ba zata ci ba saboda a gidansu saman dining table ake jera mata abinci kala goma sha biyar, sai ta za6a ta darje, hatta abincin ma abaki masu aikin gidansu suke bata tana ci” gaba ษ—aya ta rikita su da maganganunta, sun gaza gane inda ta dosa,

Duk yadda suka so su lallasheta akan taci abinci taฦ™i ci, tace musu dole a kira kukun da suke girฦ™a abinci a makarantar ta, don ta faษ—a musu kalar wanda ake girka mata agidan daddynta, idan har suna son zaman lafiya, idan ba haka ba zata yi magana da shugaban makarantar yayi musu magana, ” Su angel sun sha dariya kamar zautattu jin wani sokiburutsi na Unaiza, Sun maida ta mahaukaciya, ta zamar musu tamkar Comedy, kuma ita har ga Allah dagaske take basu Umarni, Rashin sani yafi dare duhu.

Lokacin da dare Ya tsala, Babu wanda Ya runtsa acikinsu daga su har sabbin prisoners ษ—in saboda rigimar Mahaukacin yaron nan MAJNUN! ya addabi rayuwarsu tun da ya farka daga bacci, Ya dinga Tsalle tsalle har saman gadajen su, Ya hanasu sakat, Su azeeza sun sha kuka saboda ฦ™ululun baฦ™in cikin daya dasa musu, Har bugunshi suka so suyi amma Danish ya hana su, ya basu haฦ™uri akan kada su ta6a shi yaro ne, ba dan sun so ba suka Haฦ™ura suka ฦ™yale shi, Taimakon da Allah yayi musu yaron baison duhu, Sun gane hakan ne lokacin da Danish Ya sauko daga saman gadonshi yaje ya kashe floor lamps ษ—in ษ—akin, Duhu ya gauraye ko’ina, ai kuwa ya birkice musu ya dinga kuka yana fadin su taimaka mashi, dodo zai cinye shi, angel tace munafuki ai kaine dodon daka addabi rayuwarmu ashe kana magana, nayi tunanin kurma ne kai.

Daฦ™yar Danish Ya ruฦ™o hannun shi Cikin duhu Ya kai shi saman gadonshi ya haye Yana faman sauke ajiyar zuciya, ganin ya samu natsuwa ne, ya tambaye shi ya sunanshi, Muryarshi adisashe ya ce”CHINONSO” jinjina kai Danish yai kafin ya miฦ™e ya rufa mishi bargo saman Jikin shi.

A washe garin ranar da aka kawo musu sabbin prisoners, lokacin Da Giants suka zo kawo musu Abinci, Sun ga haukan da basu ta6a gani ba, wato unaiza ce ta tsare giants tana zazzaga musu masifa akan su bi tsarinta, na gidan daddynta, hada ฦ™oฦ™arin ษ—auko jotter acikin school bag ษ—inta tare da biro ta rubuta musu list na abunda take so adinga girka mata tana ci, bayan ta gama ta je gaban su ta miฦ™a musu paper ษ—in data yago cikin jotter din, tace dasu su kar6a, Kamar gumaka babu wanda ya motsa a cikin su,
Su haris suna ta ฦ™oฦ™arin fahimtar da ita akan ta matsa daga gabansu basa magana, amma taฦ™i sauraransu, ba don Allah yasa Naufal Yaje ya janyeta ba, da ranar ta yabawa aya zaฦ™inta, don wlh mazga zata sha awurin su, don basa ษ—aukar raini.

A taฦ™aice Cikin kwana uku sai da suka fita hayyacinsu, Akan mutun biyun nan Unaiza ฦดar gidan daddy da kuma Majnun Chinonso,

Wata sabuwar rigima ta unaiza, ta faษ—a musu cewa ita fa Ta saba agidansu masu aiki suna yi mata tausa, don haka suma dole suyi mata, Kuma idan zata kwanta bacci, Da pillow uku take kwana saman gadonta, ta saba duk in zata kwanta, tana ษ—aura kanta saman pillow, ษ—aya kuma A tsakankanin ฦ™afafuwanta, Cikon na Ukun A ฦ™irji take rungume shi, Ba tare da sun yi mata musu ba, Su Parveen su ka yi mata tausa, Lokacin da dare ya yi Danish da Mubeen suka bata pillows ษ—in su don ta kwanta kamar yadda ta saba yi agidansu, Idan fa tace su yi mata abu su ka ฦ™i yi mata, Kamar ฦ™aramar yarinya haka zata zauna tana raira musu kuka, waya ga shagwa6a66a

Haris yace”Su ฦ™yaleta Ai wadda tafita iya masifa tazo kuma ta miฦ™a wuya sun yi rayuwa da daษ—i da ba daษ—i balle kuma ita, ” Wato yana magana akan angel, sai dai fa akwai banbanci sosai tsakanin Angel da Unaizah.

Ranar da haฦ™urinta ya ฦ™are, ganin anฦ™i yi mata abunda take so, Tace musu zata kashe kanta, a lokacin sun ษ—auka wasa take Yi ashe dagaske take, dama irinsu basu Cika imani ba, basu da tawakkalli, gata dai da sunan musulmai amma babu musuluncin acikin zuciyarta,

Suna zazzaune acikin ษ—akinsu kamar masu zaman makoki, ba zato ba tsammani suka soma Jin Ihunta Acikin Toilet, Da gudun gaske suka faษ—a Sashen makewayin nasu, sai dai koda suka isa ta datse ฦ™opa, Suka dinga bugu taฦ™i buษ—e musu, Danish ne ya bugi ฦ™opar da hannayenshi nan take ta buษ—e, Suna Shiga Ciki suka same ta kwance ฦ˜asa Tana burgima, gefenta ledar detergent ce da tasha duk don ta kashe kanta, Rai a6ace Danish yasa hannu ya damฦ™o damtse hannunta, ya ษ—ago da ita, tana ta faman shessheฦ™ar kuka, Da gwiwar hannun shi ya daki bayanta, gaba ษ—aya saida ta amayar da abunda tasha kaf ษ—insa, cikinta kamar zai 6alle saboda ษ—amewar da yayi, Idanuwanta su kayi luhu luhu, Saboda tsabar kuka hada majina ta hanci ta baki,

Angel ce ta taimaka mata wurin wanke mata fuskarta, ta kuskure bakinta, kafin ta ruฦ™ota ita da hanna suka shigo da ita Cikin ษ—akin a saman gadonta suka kwantar da ita, sai nishi take yi, launin idanuwanta sun ciza, daga gani tana acikin mawuyacin hali, zazza6i ya rufe jikinta ta ko’ina, A kewaye da gadon Su angel suka zazzauna tare da Danish, Sauran ฦณan uwan nasu suna atsaye suna kallonta,

“Yanzu idan kika kashe kanki wa kika yi ma asara”? Haris ne yai mata maganar, saboda ฦ™arfin hali tace mashi”bansani ba, Ni ba ruwana da kowa, Ku ฦ™yale ni ku bar ni inyi rayuwata, Na tsani ganin ku, bana son Zama acikin ku, i just wanna Go home” Jinjina kai su ka yi, Haris ya kuma cewa”kin ษ—auko ta da zafi, Ae duk wanda ya shigo kurkukun ฦ™addara, To ya shiga kenan ba hanyar fita, Zaifi ki kwantar da hankalin ki, ฦณar gidan daddy ki yi rayuwarki Cikin salama, kamar yadda kika ga muna yi,”

Wani irin kallon harara ta dinga jefa ma haris da yae maganar, Cikin harshen turanci ta zazzage shi tas hada yi mishi sharrin halittarshi wai baฦ™i mummuna kamar buri, A fusace Deeja ta ษ—aga hannu zata kwashe ta da mari Danish yai saurin ruฦ™o hannunta, Suka haษ—a ido ya girgixa mata kai alamar karta mare ta, zame hannu deeja ta yi yayin da take kallon ฦณar gidan daddy dake kwance saman gadonta, Wani irin kallon tsana take binsu dashi, angel tace”duk wani abu da kike taฦ™ama dashi muma muna dashi, Idan hasken fata ki ke taฦ™ama dashi Muma duk farare ne balle kice xaki nuna mana wariyar launin fata ehe, Sannan kuma idan gashi ne ki kalli kaina da kyau, Nesa ba kusa ba, Nafi ki tsayin gashi da yawa, haka zalika idan launin ฦ™wayar ido ne, Na ki blue nawa Gray, Idan wayewa ce, yadda kike taฦ™ama da daddynki, Nima haka na taso Gidan daddyna, Yana gatanta ni duk da bamu da ฦดan aiki kamar yadda kike faษ—in akwai su a gidan ku, Shawarar da zan baki shine idan har kina son xaman lafiya to kija baki kiyi shiru ki rungumi ฦ™addararki, Bawai kice xaki ฦ™i cin abinci ba, ko ki ce zaki kashe kanki, Domin kuwa babu wanda ki kayi ma asara face kanki. hatta shi daddyn naki da kike taฦ™ama dashi Yana can hankalin shi kwance ya sadaukar dake zuwa ga rayuwar ฦ™unci da takaici, saboda ya samu abunda yake so………” tun da angel ta doma magana, ฦณar daddy ta zazzaro idanuwanta akan fuskar angel, duk da bata fahimci abunda take nufi ba amma ta shiga ruษ—ani sosai, Muryarta na rawa tace”Naji kince daddy na ya sadaukar dani what does that mean”? Angel na ฦ™oฦ™arin yi mata bayani, Danish yae mata gyaran murya nan take ta fahimci me yake nufi, Wato kada ta faษ—a mata.

A tsanake Danish Ya soma yi mata magana

“Yanzu baki da ฦ™oshin lafiya, ga shi ko abinci kin ฦ™i ci, why? Ki faษ—a mana me kike so muyi maki wanda zaisa ki saki jiki damu” yanayin yadda yake yi mata magana cikin sigar lallashi ba ฦ™aramin fusata angel yae ba ganin yadda Unaiza ta tsare shi da idanuwanta har wani lumshe su take yi akan fuskarshi, cikin shagwa6a tace mashi”indai zai bata abaki, zata haฦ™ura taci abincin ko ba daษ—i” sakin baki angel tai tana kallonta,

Shi ko hada ruฦ™o hannayenta acikin nashi, saboda jin ta amince indai zai bata abaki, yace mata”ae ba wani abu bane, fiye da haka ma zai iya yi mata, indai zata saki jiki dasu ta xauna batare data ฦ™ara yunkurin kashe kanta ba”

Tun kafin ya rufe baki, Ta miฦ™e zaune tana faman cizon la66anta, Su haris su ka baza ido suna kallon ikon Allah, duk wannan budurin da suke yi, Majnun yana kwance daman gadonshi yana bacci, Shiyasa suka samu salama.

Hankalin Angel fa ya tashi ganin Unaisa ta kwantar da kanta saman ฦ™irjin danish, Hada sanya hannu biyu ta ฦ™ankame shi, tana faษ—in”In dai ya ษ—aukar mata alฦ™awarin zai yi mata komai take so, to zata daina tunanin kashe kanta, kuma zata xauna dasu lafiya” tana magana tana tura mashi ฦ™irjinta ana shi, tsabar takaici Ya hana angel buษ—e baki tae mgana, Ba ita ba hatta su Hibba sun lura da irin yadda take matse jikinta dana Danish, Lamarin ya ษ—aure musu kai matuฦ™a, sai kace ba ita bace take ฦ™oฦ™arin kashe kanta ba, ta zaฦ™e sai zuba ma Danish shagwa6a take yi, ba lallai su fahimci me take so ba, saboda su awurinsu bawani abu bane don mace ta haษ—a jikinta da na Namiji shiyasa basu kawo komai aransu ba, shi kanshi Danish ษ—in Bai janye ta daga Jikin shi ba, Duk da atsorace yake da irin mugun kallon da angel take jefa mashi, Ta riga ta gane ainihin wacece yarinyar, tantiriyar ฦดar iskace tazo musu da bidi’a……

(Yakamata angel ta koya mata Sunnah๐Ÿคฃ)

*in sha Allah, Idan Allah yakaimu na Kammala Free pages of Takun farko, zan ษ—auki hutu, kafin acigaba da middle step, saboda in samu natsuwa kafin in dasa, ba jimawa zanyi ba, ฦดar tazarace, Ga masu son cigaba da Karanta Littafin kurkukun ฦ™addara 500 ne kacal, Labarin yanzu nake Cikin rubuta shi babu Complete sai dai ka biya asanyaka agroup inda zaka dinga samun update akai akai, Inka biya za’ayi adding naka a paid group kuma za’a sanyaka a comment section, Sa’annan Ba’a share Ko yin forwarding duk wanda yayi gigin fitar da littafin, akwai ta inda zamu ga sunan shi da alamar yayi forwarding to zamu cire shi a group ne๐Ÿ‘Œ Kuma yaja ma kanshi zamu ษ—auki mataki๐Ÿ‘Œ*

*Littafin Kurkukun ฦ™addara 3 part ne, Yanzu muna gab da ending na Takun farko free kenan, Sai kuma Takun tsakiya wanda ya kasance na kuษ—i ne, da takun karshe duk akan 500 zaku karanta shi*

*Ga wanda ya shirya Yin payment, ga details nan, Idan ka tura kuษ—in zaka bamu shaida, Bamu kar6ar kati, Ta bank ake turawa ko ta pos, In yaso saika ษ—auko hoton reciept ka tura mana*

*3196407426*
Bature Hafsat Muhammad
First bank

*Zaka tura da shaidar Biyanka ta wannan Numbers ษ—in (0816985 6268) ko kuma ta (08103884440)*

No comments

Powered by Blogger.