Bad Boys 34
A ɗarare ya masu sallama, Ambassador da be waye shi ba ya amsa with a broad smile “Zo ga waje ” ya nuna masa kujera ,shikam Ya Sheikh yanda kasan an aiko masa da saƙon mutuwa haka yayi kicin kicin da rai .
“Gata nan a bayana ” Adnan ba hausa ,baisan baƙar magana ba ,sai muskutawa yayi yana leƙen bayan ya Sheikh
“Sharaff…”
“Food is readyy…” Salima ta fito tana faɗa cikin barkwanci tayi gayunta da ɗaya daga cikin kayan da Adnan ya Bata ,tana ganin Adnan zaune da manyan jakuna a gabansa tasan ba lafiya a sanyaye ta cigaba da sakkowa,daga matakalen benen
“Dr kaine ? Amma ynz ka shigo ko?” ta masa magana da larabci a sanyaye kamar tasan ana tsaka da cin masa mutuncine.
Gyada mata kai yayi fuskarsa kadaham kadaham
Miƙewa yayi ya cicciɓi madaidaicin jakan gabansa ,ya miƙa mata
“Happy wedding anniversary…Allah ya ƙaro zaman lafiya a aurenku ya baku zuriya masu Albarka these are the little gift I can offer…” ya nuna mata tarin kayan da ya zo dasu bayan ɗan madaidaiciyar jakar da ya bata
Cusa kanta tayi ta leƙa ,agogone na mace da namiji iri ɗaya sai wani box ɗin ɗan kunni da yarin gold”
Ihun murna ta fashe dashi “Yeeeeh ta runtuma gaban Sheikh tana nuna masa gift din da aka basu tare dukda sauran masu nauyin batasan ko menene ba amma basu wuce sutura ,don shine abinda Salima take ƙaranci.
Ba kunya ya Sheikh ya washe baki “Kamfanin Rolex ne ko me? Kai wanann agogo da ɗaukan ido yake ,ya akayi kasan yau ne ma ranar….” buge masa hannu ambassador yayi ,wanann yasa ya Sheikh shiru yana zare ido .
Waigawa Salima tayi ya kalli Adnan “Ya akayi kasan yau anniversary dinmu?”
“A IG Naga post din hotunan bikinku” girgiza kai tayi cikin jimami yana tuno mata da memories.
Kauda kai yayi “Bari inje ko?🤨”
“Aah no abincinmu a table tare zamuci duka” Ambassador ya karɓe da sauri.
Ya Sheikh ji yayi kamar ya kashe Ambassador don haushi ,zaija a cinye masa abincin da yayi budgeting zasu ɗumama da safe,in yayi ragowa.
“No Yanzu na dawo daga Office inaso inje inyi wanka”
Sarai Adnan da Salima duk sun lura da halin da ya Sheikh ya shiga ,don Adnan ya gama gane Sheikh ba ƙaramin zumbuli bane ƙarewar rowa.
“Bari inje inyi wankan zan dawo” Ya amsa tayin Ambassador da gayya ,yau saidai in yaci abincin Ya Sheikh ya hadiyi zuciya ya mutu.

Leave a Comment